Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sallami manyan jami'an tsaron kasar.
Shugaba Buhari ya kori hafsan hafsonshin rundunar sojin sama da ta kasa da ta ruwa.
Wadanda aka kora su ne: Air Marshal Alex Badeh, Janar Kenneth Minima da Rear Admiral Usman Jibrin da kuma Air Vice Marshal Adesola Amosun.
Wata majiya a fadar shugaban Nigeria ta shaida wa manema labarai cewar nan gaba a ranar Litinin za a sanar da sabobbin manyan hafsoshin tsaron.
An dade ana saran shugaba Buhari zai kori manyan hafsoshin tsaron a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a cikin kasar.
A cikin kwanaki goma da suka wuce an kashe mutane fiye da 220 a Nigeria sakamakon hare-haren Boko Haram.
Tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ne ya nada su.