Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sallami manyan jami'an tsaron kasar.
Shugaba Buhari ya kori hafsan hafsonshin rundunar sojin sama da ta kasa da ta ruwa.
Wadanda aka kora su ne: Air Marshal Alex Badeh, Janar Kenneth Minima da Rear Admiral Usman Jibrin da kuma Air Vice Marshal Adesola Amosun.
Wata majiya a fadar shugaban Nigeria ta shaida wa BBC cewar nan gaba a ranar Litinin za a sanar da sabobbin manyan hafsoshin tsaron.
An dade ana saran shugaba Buhari zai kori manyan hafsoshin tsaron a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a cikin kasar.
Title :
Buhari ya kori manyan jami'an tsaro
Description : Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sallami manyan jami'an tsaron kasar. Shugaba Buhari ya kori hafsan hafsonshin rundunar sojin sama ...
Rating :
5