Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce kasarsa ce ya kamata ta rike shugabancin rundunar hadin-gwiwa da za a kafa domin yaki da kungiyar Boko Haram.
A jawabinsa lokacin taro da sauran shugabannin kasashe biyar a Abuja, Buhari ya ki amincewa da bukatar a dinga karba-karba na shugabancin rundunar tsakanin Nigeria da Chadi da Kamaru da Nijar da kuma Benin.
"Akwai shawarar a dinga yin kwarba-kwarbar shugabancin rundunar na tsawon watanni shida tsakanin kasashe biyar, amma ina ganin cewar hakan zai shafi aikin yaki da 'yan ta-da-kayar-baya," in ji Buhari.
A cewarsa, dan Nigeria ne ya kamata ya jagoranci rundunar na tsawo lokacin yaki da Boko Haram.
Shugabannin kasashen biyar na fatan fitowa da wasu sababbin manufofi game da yaki da Boko Haram da kuma duba yanda za su inganta tattalin arziki da kuma abubuwan inganta rayuwar da suka lalace a yankin da rikicin ya yi wa kaca-kaca.
Shugabannin da suka halalrci taron su ne Muhammadu Buhari na Najeriya da Muhammdou Issoufou na Njira da Idris Deby na Chadi da Boni Yayi na jamhuriyyar Nijar da kuma wakilin shugaban kasar Kamaru Paul Biya.
Title :
Buhari ya bayyana matsayinsa kan Boko Haram
Description : Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce kasarsa ce ya kamata ta rike shugabancin rundunar hadin-gwiwa da za a kafa domin yaki da kungiyar B...
Rating :
5