Rahotanni daga jihar Yobe na cewa akalla mutane bakwai ne suka rasu lokacin da wani bam ya tashi a wata mota a Damaturu babban birnin jihar.
Wani jami'an 'yan sanda ya tabbatar wa da BBC abkuwar lamarin.
Ya ce cikin mutanen da suka mutu, biyar mutanen da suka kai harin ne, yayin da 'yan sanda biyu suka rasa ransu.
Akwai wasu mutane da suka samu raunuka lokacin da bamb din ya tashi a cikin wata mota kirar Jeep a wurin tantance ababen hawa da jami'an tsaro suka kafa.
Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a garin.