Mayakan Boko Haram sun kai hari a garin Buduram kusa da Baga da ke karamar hukumar Kukawa a cikin Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, kuma sun yi mutane kimanin 10 yankan rago tare da kona gidaje.
Mayakan sun kashe mutane tare da tursasa wa wasu da dama ficewa garin da ke kusa da Baga, kamar yadda wani da ya tsira daga harin ya shaida wa manema labarai.
Mayakan na Boko Haram sun shiga garin Doro zuwa Bunduram a cikin Daren Litinin, inda suka farwa mutanen garin da harbi kan mai uwa da wabi.
Yawancin wadanda aka kashe masu kamun kifi ne a kusa da tafkin Chadi. Wasu da dama kuma sun fada cikin ruwa domin tsira da ransu.