Mataimakin shugaba Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce wani rahoton sirri da suka samu ya nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram za su fara kai wa manyan mutane hare-hare.
Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan watsa labarai ya fitar ta ce mambobin kungiyar ta Boko Haram za su fara yin shiga irin ta baban-bola domin zubar da shara mai dauke da bam a gidajen manyan mutane.
A kwanakin baya ne mataimakin shugaban na Najeriya ya kai ziyara arewa maso gabashin kasar domin jajanta musu kan hare-haren da Boko Haram ke kai wa a yankin.
Farfesa Osinbajo ya bukaci kafafen watsa labarai su zage-dantse wajen wayar da kan 'yan kasar kan irin dabarun da Boko Haram ke amfani da su domin kai hare-hare.
Wasu alkaluma sun nun cewa kungiyar ta kashe fiye da mutane 17, 000 tun da ta kaddamar da hare-hare a shekarar 2009, sanna ta raba miliyoyin mutane da muhallansu.