Ina yi muku Wasiyyah tare da ni kaina, cewa Muji tsoron Allah... sannan mu dubi wadannan tambayoyin kuma muyi tunani akansu:
Sau nawa a kullum kake tsayawa kayi tunani akan ranar mutuwarka, Ajalinka, da kuma makomarka??
Sau nawa a kullum kake tsayawa kayi tunani akan Kwanciyar Qabarinka, da duhun Qabari da tsananin Matsinsa da zafin cikinsa??
Sau nawa a kullum kake tsayawa kayi tunani akan ranar Hisabi, tsayawarka agaban zatin Ubangiji, Karbar takardarka ahannun dama, ko haggu (Allah shi kiyayemu).
Sau nawa akullum kake tsayawa kayi tunani akan Siradi da bala'in da yake dauke dashi, da kuma Jahannama da Kayan Masifar da take Qunshe dasu???
Idan har baka samun lokaci a kullum domin yin tunani akan abubuwan nan da ba lissafa, to hakika dole ka Qirga kanka acikin Gafalallu, rafkanannu, wadanda basu san kansu ba, ballantana su gane girman Ubangijinsu.
Idan kuma kana samun lokaci domin tunani akan wadannan abubuwan, to mai yasa ba zaka gyara ayyukanka ba??
Mai zai hana ka shagaltu da Kanka, ka gyara laifukanka, ka nemi gafarar zunubanka, sannan ka yawaita ayyukan alkhairi domin samun kubuta daga Azabar lahira!!!
Nasiha ce nayi ma kaina... da kuma dukkan mai hankali, irin hankalin da yake da amfani ga masu Shi.