Nan yashiga yiwa mutune bayani wai yaga mun fado daga bokanya kufana ta kawomu nan sanadiyar rashin kunyarda biyu daga cikinmu suka mata nan diyan hanjinmu suka kada muka shiga kallon kallon wato bokanyace muka hadu da ita nan nadinga kuka itakuwa dan me xata mana haka bayan tasan mu ba irin halittarsu bace dama kashemu tayi muka huta yafi wannan wahalar
Nan yacigaba dayake cikin turanci yake maganar tace zata bayyana domiin ta yanke masu hukunci saboda sun bata mata rai sosai
duk maganarda yake yana gurfanene gaban dattijonan wanda naji yana Kira king laihanu wato sarkine wanan hmmm yana gama fada saiga wani irin haske take ta bayyana tana sauka kamar tsuntsuwa,take gurin yadauki kuwa kufana "kufana"kufana"har ta sauko tana murmushi taje gaban king laihanu tana gaisuwa nan tashiga basu lbrn yadda ta hadu damu da irn walakancin da su anty salma sukayimata
Take aka fara jifarmu nan tayi umarni d hannunta ban anakraba sai gani gabanta sukuwa su anty khadeeja aka cigaba d jifansu duk anfitarmasu da jini ni kuwa sai kuka nake ina rokan suyi hakuri amma INA dole na durkusa gaban kufana INA rokonta da tayi hakuri naci SAA kuwa ta saurareni tayi umarni da sudaina jifansu aikuwa da guduna na isa gurinsu duk sun galabaita jikinsu da fuska duk jinine hmmm yan gatan su mummy ne wai haka rugumesu nayi INA shafemasu jinin fuskokinsu INA kuka anty khadeja ce tayi karfin halin magana iki kiyi hakuri da irin halinda muka sakaki nasan mu tamu takare idan kika samu komawa duniyarmu ki rokamana su daddy su yafe mana kanji yaune irin ranarda suke mana gudu ashe wulakanci bashida kyau wani k kewa ka gama lpy wani kam""" shuru tayi takasa karkare maganr saboda Adana,itakuwa anty salma banda kuka ba abunda take idonta cike d nadama,nikuwa sai rubxarkuka nake ina baxaku mutu kubarniba tare xamu mutu daku nima duk takshe Ku saita kasheni, baxan iya jurar ganinku cikin wahalaba,.
Y Allah kamana mafita ta alkahairi da karfi nake fadar haka duk abunnan da muke kallonmu kawai suke
Nan kufana taci gaba da cewa xani hukuntasu hukunci mafi muni duk da mu a duniyar bamu horon kisa amma xan ladabbtasu tayadda baxasu sake marmarin wulakanta waniba, saboda haka na diba masu shekara talatin, INA hukuntasu, sannan na maidasu duniyarsu, kekuma xan maidaki duniyarku domin kikai labr, da guduna naje gurinta narike kafarta mai taushin gaske INA rokonta da ta barmu mutafi amma INA taki nan nace nikuwa baxanje ko ina ba ina nan tare da yan uwana haranan da shekara talatin idan Allah ya kaimu, da kyar ta amince nan su khdeeja sukayi sukayi da inje ta maidani naki,kije iki kinsan iyayenmu xasuyi rashinmu amma wata kila idan suka ganki xasu rage wani abu, ba llalle ne mukai shekara talatin da rayuwaba, koda munkai kina ganin nanda shekara talatin xamu isake yan uwanmu da rayuwa,anty salma ko shekara darine xan tsaya koda ko xan rasa rayuwatane baxan iya tafiya nabarkuba baxan iyaba,nan nakara fashewa d kuka, ikin daddy kibarmu muda muka ja ruwa su jamu karki lalata rayuwarki yadda tamu ta lalace,anty khadeeja ke maganar,itakuwasalma cetake Allah sarki gwaggo dama mundauki shawarta, nan fa mukayita kuka har akaxao aka wuce dasu anty salma tofa nan sabon kuka yatshi, nikuwa kyakykyawar matanna wacce naji suna kirada princess ikahala ita taxo tace xata je dani gurinta da haka aka rarrabamu tofa muje xuwa.
Da haka aka rabamu, akatafi dasu nima princess ikhala tawuce dani, nan ma nasha kallo amma dayake tunanin yanuwana na raina ban tsaya wani kalle kalleba, gashi su daddy su inata tunosu ko wane hali xusu shiga idan suka nememu suka rasa, sabon kika nasake rusawa, nan ikhala taxo tana lallashina dayake kufana ta gaya mata ta kula dani sosai, hannunta mai laushi ta axa a kafadana tana lallashina nan na ture hannunta ina kuka.kibarni nayi kukana idan har baxaku sake yan uwana ba ki kyaleni.
Duk abunda na fada taji dayake turanci nayimata,
Hakuri tacigaba da bani, cikin harshen turanci take maganr sunana ikhala kamar yadda kika ji ni yar sarki ce, kuma inda Yaya prince kam eer, gwarxon namijine gashi kyakykyawa, yanxu haka yanacan gurin yaki da wadansu dodonni dake mana barna anan garin, wannan garin dakike gani babban garine ya samo asaline daga mutun biyu, matsafane na gaske aka korosu daga birnin sin sai suka yi tafiya mai nisa sannan suka kafa wannan birnin har xuwa yanxu, nan nadago na kalleta cikin mamaki nace mata shin yanxu dai dai wani garine birnin nan naku na matsafa yake,murmushi tayi sai da tsdade sannan tace yana gaba ga birnin sin, ido naxare tareda dafe kirjina INA salati ikhala kina nifin yanxu muna kusaga bangon duniya.kwarai kuwa hakane,NaN nashiga rero sabon kuka, kinga kiyi shuru kigaya mani duk abinda kk so xan maki idan baifi karfinaba, saboda naji kawai INA kaunarki da tausayinki, ajiyar xuciya nayi, nace nidai abu daya xakimun nasan kina tausayina kuma kina kaunata ki maidamu duniyarmu nida yan uwana baxamu iya rayuwa da kuba,