Wasu mata 'yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a wararen binciken mutane kafin su shiga filin Sallar Idi a Layin Gwange, a Damaturu, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 12.
Hare haren biyu sun auku ne adai dai lokacin da musulmai a birnin ke shirye shiryen zuwa masallatai domin Sallar Idi ta karamar Salla.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce daya daga cikin matan yarinya ce mai kimanin shekaru 10.
Kanar Kukasheka ya ce harin na farko ya kashe mutane 7, yayin da harin na biyu ya kashe mutane 5.
Ya ce rundunar sojin kasar ba zata girgiza ba a kudurinta na kawar da masu ayyukan ta'addanci a kasar.