Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nijeriya na cewa an samu fashewar bam a wata majami'a a Unguwar Tudun Wada.
Bayanai dai na cewa an dasa bam din ne a cikin ban-daki na majami'ar a cikin leda, kuma da daya daga cikin jami'an tsaron majami'ar ya ga ledar sai ya dauka ya jefar, nan take kuma bam din ya tarwatse.
Haka nan kuma kwararrun jami'an tsaro kan sha'anin bama-bamai da suka ziyarci wurin, sun gano wani bam din da aka dasa kusa da majami'ar, a cikin buhu kana suka tayar da shi, amma dai babu hasarar rayuka ko jikkata.
Wannan lamari a Majami'a a birnin Jos dai, ya faru ne kimanin mako guda da aka samu wasu hare-haren bama-bamai da bindiga a wani Masallaci da kuma wani wurin cin abinci a birnin na Jos, inda mutane kimanin hamsin suka rasa rayukansu wasu fiye da saba'in suka jikkata.
Title :
Bam Ya Fashe A Cocin Ecwa Dake Birnin Jos
Description : Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nijeriya na cewa an samu fashewar bam a wata majami'a a Unguwar Tudun Wada. Bayanai dai...
Rating :
5