Mahaifin tsohon mai ba wa tshohon shugaban Najeriya shawara kan tsaro, mai alfarma tsohon Sarkin Musulmi na 18 a Nigeria, Alhaji Ibrahim Dasuki, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami'an tsaro suka shiga gidansa na Sokoto inda suka yi binciken kwakwaf.
Dasuku ya ce bai kamata jami'an tsaro su shiga gidansa ba tare da neman izininsa ba, saboda akwai bambamci tsakaninsa da dansa Kanar Sambo Dasuki.
Jami'an hukumar farin kaya ta SSS dai sun kai wani samame gidan Kanal Sambo Dasuki, a Abuja da kuma gidan mahaifin nasa, Alhaji Ibrahim Dasuki, a Sakkwato, ranar Juma'a.