Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai nada ministocinsa ne a watan Satumba mai zuwa.
Ya bayyana haka ne a wani sharhi da ya rubuta a jaridarWashington Postta Amurka.
Shugaba Buhari ya ce ya yanke shawarar nada ministocin a watan Satumba ne domin ya samu damar gyara harkokin gwamnatin kasar.
A cewar sa, yana sane da korafe-korafen da wasu ke yi na jan-kafar da yake yi wajen kawo sauyi a kasar, yana mai cewa dole ne a yi taka-tsantsan wajen gudanar da sauye-sauyen.
Shugaba Buhari ya ce ko shugaban Amurka Barack Obama sai da ya kwashe wata da watanni kafin ya nada ministoci, yana mai yin kira ga 'yan Najeriya da su yi hakuri, domin kuwa "sannu ba ta hana zuwa"