Wata kotu a Libya ta yanke hukuncin kisa a kan dan gidan marigayi Moammar Gaddafi, Saif al Islam da wasu mutane takwas.
Wasu daga cikin mutane takwas din da kotun ta yanke wa hukuncin kisa su ne Abdallah al-Senousi, tsohon shugaban hukumar leken asiri da Al-Baghdadi al-Mahmudi, tsohon Firai Mininstan kasar.
Kotun ta ce ta samu mutanen ne da aikata laifukan yaki a lokacin juyin-juya-halin da ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin Moammar Gaddafi a shekarar 2011.
Kotun ta kuma yanke daurin shekaru da dama a kan wasu tsofaffin jami'an gwamnatin Gaddafi.
Saif al-Islam dai ba ya kotu a lokacin da aka yanke hukuncin, koda yake ya bayar da shaida ta hanyar bidiyo.
Wasu kungiyoyin masu tayar da kayar baya ne ke ci gaba da tsare shi a garin Zintan.