Majalisar masarautar Zazzau a jihar Kaduna ta ce bana ba za ta yi bikin hawan Sallah kamar yadda aka saba yi a duk shekara ba, bayan kamalla azumin Ramadan.
Majalisar karkashin jagorancin, Mai Martaba Alhaji Shehu Idris a cikin wata sanarwa, ta ce an dakatar da bukukuwan hawan Sallar ne saboda dalilai na tsaro.
A cikin wannan watan ne aka kai harin kunar bakin wake a Sabon Garin Zaria inda aka hallaka mutane 20, hakan kuma ya janyo soke bikin hawan Sallar.
Baya ga masarautar Zazzau, an dakatar da shagulgulan Sallah a wurare da dama a arewacin Nigeria saboda yadda ake fargabar ayyukan 'yan Boko Haram.
A cikin 'yan shekarun nan hare-haren 'yan Boko Haram sun jefa jama'a a cikin hali na tsoro abin da ya rage armashin bukukuwan Sallah a kasar.