Maganin riga kafin cutar zazzabin cizon sauro wato Maleriya na farko ya cika muhimman ka'idojin da aka shimfida kafin a amince a fara amfani da shi a kasashen Afirka.
Riga kafin zai yi matukar rage yiwuwar kamuwa da Maleriya mai tsanani tsakanin yara da suka yi amfani da shi sau hudu.
Hukumar sa ido a kan magunguna ta Turai ta amince da riga kafin bayan tantance ingancinsa.
Sai dai riga kafin ba zai amfani jarirai ba, domin haka ne ma hukumar lafiya ta duniya, WHO take da dan shakku a kansa.
Karuwar amfani da gidan sauro da aka yi wa feshin magani, cikin 'yan shekarun nan ya rage rabin asarar rayuka da aka samu sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro.