Kotu a birnin Alkahira na Masar ta sake dage zaman shari’ar da akewa hambararren zababben shugaban Masar na farko Muhammad Mursi bisa zargin sa da yiwa kasar Qatar aiyukan leken asiri.
Kotun hukunta manyan laifuka dake birnin Alkahira ta dage karar zuwa ranar 21 ga watan Yuli.
A watan da ya gabata, wata kotun daban ta yankewa Mursi hukuncin kisa sakamakon tuhumarsa da laifin fasa gidan yâri a lokacin zanga-zangar shekarar 2011. Bayan hukuncin na kisa, akwai kuma kotun da ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
A ranar 3 ga watan Yulin shekarar 2013 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Mursi a Masar