Gwamnatin Zimbabwe ta fara neman wani mutum ruwa-a-jallo bisa zargin kashe wani fitaccen zaki a gidan ajiye namun dajin kasar.
Anar zargin mutumin da bai wa masu kula da gidan ajiye namun dajinHwangecin hancin sama da $50, 000 domin ya kashe zakin mai sunaCecil the lion.
Wani mai kula da namun dajin Johnny Rodrigues ya shaida wa manema labarai cewa an harbi zakin ne da kwari-da-baka da kuma wata karamar bindiga, sannan aka yanka namansa.
Zakin, mai shekaru 13, yana cikin zakunan da masu ziyartar gidan namun dajin suka fi so.