Rahotanni daga garuruwan Ngamdu da Damasak na jihar Borno na cewar mayakan Boko Haram sun kaddamar da hare-hare.
Rahotanin sun kuma ce an samu hasarar rayuka kuma an kona gidaje da dama a garuruwan Ngamdu da kuma Damasak.
Wadanda suka sha da kyar a Ngamdu sun tsere zuwa wasu garuruwan da ke Borno da kuma Yobe.
Dan majalisa da ke wakiltar mazabar Kaga da Gubio da kuma Magumeri, Honorabul Mohammed Sanda ya shaida wa mane ma labari cewar, "da misalin karfe 5 na ranar Talata, 'yan Boko Haram suka tare hanyar Maiduguri zuwa Kano inda suka kona motoci suka hallaka mutane."
"Ba mu san adadin wadanda suka kashe ba. Amma an ce sun kashe mutane sun fi 20," in ji Sanda.
Dan majalisar ya bukaci jami'an tsaro su kara yawan dakaru domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.
Can kuma a Damasak, lamarin ya sa mazauna garin Gaidam a jihar Yobe suna cikin zaman zullumi.