Rundunar 'yan sandan Daular Larabawa ta
ce ta kama 'yan Najeriya uku masu kutse a
shafin intanet a bankunan Amurka.
An kama mutane ne bayan 'yan sandan sun
samu labarin masu aikata laifin kutsen daga
rundunar 'yan sanda ta birnin California da
ke Amurka.
Ana zargin masu laifin ne da kutse a cikin
sakonni da wuraren ajiyar kudi a shafukan
intanet, inda suke sato takardun sirrin
mutane da na ma'aikatu a Amurka.
'Yan sanda sun kai wa masu kutsen hari a
wata maboyarsu da ke masarautar Ajman,
inda suka gano jerin lambobin ajiyar kudi a
bankin intanet na mutane sama da miliyan
biyar.
Shugaban 'yan kutsen na da shekaru 24,
mabiyan sa su biyu kuma duk shekarun su
26, kuma dukkansu sun shigo kasar
Larabawan ne yawon bude ido.