Mahukunta a arewacin kasar Kamaru sun haramta sanya nikabi da kuma duk wani mayafi da zai lullube fuska ruf.
Wannan mataki ya biyo bayan harin kunar bakin waken da aka kai ne a yankin, wanda ake dora alhakin kai shi a kan kungiyar Boko Haram.
Gwamnan yanki arewa mai nisa a Kamaru, ya kuma kara da cewar an hana mutane amfani da motoci masu bakaken gilashi ko kuma hawa babura da daddare.
Dama a ranar Larabar da ta wuce ne, ita ma kasar Gaban ta haramta sanya nikabi a bainar jama'a da kuma wuraren aiki saboda hare-haren da ake kaiwa a makwabciyarta Kamaru.
Tun a watan Yuni ne dama hukumomin Chadi suka dauki irin wannan mataki.