Mutane a kalla 16 sun rasu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a garin Fotokol da ke lardin arewa mai nisa a jamhuriyar Kamaru.
Wani babban jami'in sojin Kamaru ya tabbatar wa manema labarai cewa wadanda suka rasu sun hada da fararen hula 12 da sojojin Chadi biyu da kuma 'yan kunar bakin wake biyu mata.
Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, kuma ana zargin 'yan Boko Haram da alhakin kai harin.
Hakan na zuwa a yayinda dakarun hadin gwiwa na kasashen Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin domin kawar da Boko Haram za su soma aiki a karshen wannan watan.
Bayan watan azumi ne ake saran shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari zai ziyarci shugaba Paul Biya na Kamaru domin tattauna yadda za su hada kai a yaki da Boko Haram.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.