Jami'an tsaro na hadin gwiwa a Nigeria sun gano shanu kusan 2,000 na sata a dajin Kamuku da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Jami'an tsaron sun bayyana cewa, sun gano awaki masu dinbim yawa da kuma jakuna wadanda masu satar shanu suka sace.
Jami'an sun kuma yi nasarar cafke wasu daga cikin 'yan fashin tare da hallaka wasu da dama.
Jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Kuma Niger ne suka soma aikin hadin gwiwa domin magance ayyukan wasu 'yan fashi da suka addabi dazukan jihohin, lamarin da ya janyo mutuwar daruruwan mutane.
A cikin 'yan shekarun nan dai ana yawan samun matsalar satar shanu a wasu jihohin arewacin Nigeria abin da ke jefa makiyaya cikin mawuyacin hali.