Masu bincike a Jami'ar Birmingham da ke Biritaniya sun ce sun gano wasu daga cikin takardun Al-Kur'anin da mai yiwuwa suka fi tsufa a duniya.
Masu binciken sun ce wani nazarin kimiyya da suka yi a kan takardun sun nuna cewa an wallafa su ne a karni na bakwai don haka kusan shekarun su 1,370 a duniya.
Sun kara da cewa mai yiwuwa mutumin da ya rubuta Al-Kur'anin ya taba haduwa da manzon Allah, annabi Muhammadu (SAW) ko kuwa ya taba jin sa yana wa'azi.
Binciken ya nuna cewa wani masanin tarihi dan kasar Iraki, Alphonse Mingana ne ya kai takardun Al-Kur'anin Jami'ar ta Birmingham a shekarun 1920.
Takardun Al-Kur'anin sun kwashe kusan shekaru 100 a dakin karatun Jami'ar ba tare da an kula da su ba.
Musulmai za su yi farin ciki
Wani mai nazari a kan irin wadannan takardu a dakunan karatun Biritaniya, Dr Muhammad Isa Waley, ya gano takardun Al-Kur'anin "zai farantawa Musulmai rai".
Daraktar Jami'ar da ke kula da tsofaffin takardu, Susan Worrall, ta ce "mun yi matukar farin ciki da muka gano cewa muna ajiye da takardun Al-Kur'ani mafi dadewa a duniya".
Kazalika, binciken ya gano cewa an rubuta Al-Kur'anin ne a kan fatun dabbobi.
Farfesa David Thomas da ke nazari kan addinan Musulinci da Kiristanci a Jami'ar ya ce gano Al-kur'anin "zai iya taimakawa domin gano shekarun da aka karbi Musulinci a duniya".
Ya kara da cewa "Musulinci ya nuna cewa Annabi Muhammad (SAW) ya karbi wahayi tsakanin shekarar 610 da 632, lokacin da ya yi wafati."