Mutane 56 ne suka mutu sakamakon fafatawa da aka yi tsakanin jami'an tsaron Afganistan da 'yan tawayen Taliban a larduna 6 dake jihar Faryab ta arewacin Afganistan.
Shugaban 'yan sandan Faryab Subhankul Ibrahim ya bayyana cewa, 'yan tawayen sun kai hare-hare a lardunan Almar, Kaysar, Peshtun Kot, Gurzivan, Hoca Sebzposh da Shirin Tegab inda sakamakon haka suka yi arangama da jami'an tsaro.
Ibrahim ya bayyana cewa, an kashe 'yan tawayen 44 tare da jami'an tsaro 12, inda aka jikkata wasu 32 tare da kama 'yan tawayen 2.
Ya ce sun sami nasarar kwace makamai da dama daga hannun 'yan tawayen na Taliban.
Amma kakakin 'yan tawayen Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana cewa, sun kashe sama da jami'an tsaro 20 a yayin fafatawar tare da jikkata wasu da dama.
Ya kuma ce sun kwace ofisoshin 'yan sanda da dama a yankin da lamarin ya faru.