Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce matakin da Amurka ta dauka na kin sayarwa Najeriya makamai ya taimakawa kungiyar Boko Haram wajen kara kai hare-hare.
Wata doka da 'yan Majalisar dokokin Amurka suka zartar ta haramtawa kasar bayar da makamai ga sojin kasashen da aka tabbatar suna take hakkin dan adam.
Shugaba Buhari ya ce Amurka tana aiki a kan zargin da ba a kai ga tabbatar da shi ba.
Ya yi alkawarin duba zarge-zargen da kungiyar kare hakkin bil adama taAmnesty Internationalta yi wa sojin kasar na take hakkin dan adam a yakin da ake yi da Boko Haram.
Shugaban Najeriyar ya kai ziyarar kwanaki hudu zuwa Amurka ne domin neman taimakon ta wajen murkushe 'yan Boko Haram.
Wani kiyasi ya nuna cewa kungiyar ta Boko Haram ta kashe a kalla mutane 17,000 tun daga shekarar 2009, sannan ta sace daruruwan mutane, cikin su har da matan makarantar Chibok sama da 200.