A ci gaba da ziyararsa a Kenya, Shugaba Obama ya fito karara ya nuna wa gwamnatin bukatar kawar da cin hanci da rashawa.
Ya kuma nemi a bai wa masu luwadi da madigo 'yancin yin abin da suke so.
Game da cin hancin, ya ce yana iya zama babban abin da zai hana Kenyar ci gaba, yana cewa "Wannan zai iya zama babban abin da zai yi kafar angulu ga ci gaban Kenyar da saurin da ya zarce na yanzu. Ya kuma dade wa jama'a karin hanyoyin arziki."
Sai dai yayin da Mista Obama ke yin uwa da makarbiya wajen neman 'yancin masu luwadi, Shugaba Kenyatta ya bayyana rashin daidaiton baki da Amurka a kan wannan batu.
Ya ce a wurin mutanen Kenya a kan wannan batu, hanyar jirgi daban, ta mota daban