Kakakin gwamnatin Turkiyya Bulent Arinc ya bayyana cewa, Amirka da Turkiyya zasu hada kai don yakar kungiyar ta'adda ta Daesh, inda ake jiran majalisar ministocin kasar ta sanya hannu kan yarjejeniyar.
Arinc ya ce "Ba zan fadi dukkan abubuwan dake akwai ba, amma an cimma matsaya. Daga nan kuma sai neman shawarwari da hadin kai da musayar ra'ayoyi. A saboda haka ake jiran majalisar ministoci ta sanya hannu kan takardun."
Arinc dai bai bayyana yadda za a yi aikin tare tsakanin Amirka da Turkiyya ba.