Buhari Zai yi shawarar karshen akan Wanda zasu bishi tafiya zuwa Amurka a ranar Talata 14 ga Watan Yuli.
Inji cewar Jaridar Punch, zuwa ranar Talata 14 shugaba Buhari Zai fidda sunayen wadanda zasu bishi zuwa Amurka. Kuma Buhari Zai yi shirin karshe na dabaru akan yadda tafiyar zata kasance.
Bisa shirin da akayi wanda Buhari Zai gana da Barack Obama a fadar White House a 20 ga Watan Yuli, makasudin taron dai shine yadda Amurka zata taimaka ma Najeriya wajen yakar Boko Haram, da kuma saura zantuka.
Rahotanni kuma sun nuna cewa Gwamnoni 5 za suyi ma Buhari rakiya; Abiola Ajimobi na Oyo, Rochas Okorocha na Imo, Adams Oshiomole Na Edo da wasu sauran biyu a lokacin da zasu hadu ba Obama a Washington DC a 20 ga Watan Yuli 2015.
Title :
Amaechi, Bakare kila Su Kasance Cikin Wadanda Zasu Bi Buhari Amurka
Description : Buhari Zai yi shawarar karshen akan Wanda zasu bishi tafiya zuwa Amurka a ranar Talata 14 ga Watan Yuli. Inji cewar Jaridar Punch, zuwa ran...
Rating :
5