A kasar Afrika ta Kudu, an yi wata arangama tsakanin wadansu zakuna da ragon dawa, sa’ilin da wasu motacin masu yawan bude idanu suka zo gilmawa ta cikin daji. Inda nan take zuciyoyi mafiya yawan direbobin suka daina bugawa, kowa ya fara tunanin yadda zai tsira da ransa.
Sai dai kuma daidai lokacin da ake wannan artabau tsakanin zakuna da ragon dawa, wata matashiya mai daukar hoto ‘yar kimanin shekaru 23, Carolyn Dunford, wadda ta fito yawan daukar hotuna, sai ta dauko kyamararta ta fara aikin da ta kware a kai.
Matashiyar budurwar dai ta sadaukar da ranta, inda ta rika daukar hotuna iya yadda take so domin kawai nuna bajinta a idan duniya. A cewarta, wannan wani buri ne da ta dade da shi, wanda yanzu ya cika.
Yarinyar wadda daliba ce da take karatun nazarain halayyar dabobi a makarantar Romsey, Hamsphire, tana tsakar tafiya cikin daji, kwatsam ta ci karo da wadannan zakuna, nan take ta dauka kyamararta ta fara daukar su hoto.
“Ina tunanin na yi tafiya ta kusan mintuna 45, wuraren karfe 7:45, sai na ga wasu jerin motoci suna kaucewa juna. Ina daga kai daga bayansu sai na hango zakuna guda biyu suna tunkaro inda muke, can kuma sai ga ragon dawa yana fama sheka gudu, ashe wadannan zakuna shi suka biyo, saboda haka ya gudun tsira, kafin daga baya zakuna su samu nasarar cafke wuyansa, tare da yi masa kanshin mutuwa.
“Kasancewata daliba mai nazarin halayyar dabobi, na san yadda suke rayuwa. Amma ido biyu da na yi da zaki yana farauta ba karamin farin ciki na yi ba. Gaskiya abin ya birge ni. Da ma na dade ina son ganin zakuna suna fafatawa da wata dabba a rayuwata.”