Rahotanni daga jihar Gombe a arewacin Nijeriya na cewa mutane akalla talatin ne suka rasa rayukansu, fiye da mutane dari kuma suka jikkata, a wasu hare-haren bama-bamai da aka kai a tashoshin mota ranar Laraba.
Bama-bamai na farko sun tashi ne da misalin karfe bakwai da rabi na dare, yayin da bam na biyu ya tashi da misalin karfe takwas da rabi.
Hare-haren sun faru ne sa'o'i kadan bayan da Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya ya kammala wata ziyarar aiki a jihar ta Gombe.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan yadda maharan suka tayar da bama-baman, imma dai kunar bakin wake ne ko kuma dasa bama-baman aka yi.