Daga Asma'u, Allah ya kara mata yarda, wata mace ta tambayi ma'aikin Allah ta ce, ma'aikin Allah 'Yata ce wuta ta koneta, sai gashinta ya zube, kuma zan aurar da ita, shin zan iya yi mata kari (attachment) a cikinsa? Sai ya ce: "Allah ya la'anci mai yin karin gashi da kuma wacce aka kara mata".
Bukhari da Muslim suka ruwaito.
-------------------------------------
Abu ne mai sauki aure ya mutu yayin da namiji ya fahimci an ha'ince, saboda haka tun da farko sai ayi gaskiya a fede kaza cikin gashinta kar a boye wani aibi da in ya bayyana a baya zai kawo rabuwar aure.
-------------------------------------
Ya zo cikin silsilatul ahaadesus sahiha na Albani lokacin da Umar Ibn Kattab ya je neman auren 'yar gidan Aliyu Ibn Abi Talib sai da ta bude masa kwanjinta ya gani. Hakan kuma ya zo cikin Hadisin ma'aikin Allah cewa idan mutum akwai wani abu da zai duba a mace da zai sa shi aurenta yayi hakan shari'a ta yarde masa.
-------------------------------------
Allah ya sa mun fahimta.