An karbo daga Abdullahi Ibn Mas'ud ya ce: "Allah ya la'anci mai yin zane a fuska da wacce aka yi mata, da mai gyaran gira da wacce aka gyara mata, da mai yin ushirya don kyau, da mai sauya halittar Allah." Sai wata mace ta ce masa wani abu a kan haka, sai ya ce: Me zai hana ba zan la'anci wanda manzon Allah ya la'anta ba kuma hakan na cikin littafin Allah!
----------------------------------------
Allah madaukaki ya ce: "Duk abin da manzo ya zo muku da shi ku karba, abin da kuma ya haneku ku hanu." (Suratul Hashr: 8)
--------------------------------
Bukari da Muslim suka ruwaito.