ABIN LURA... 1
Yana rikitar da mutane da dama cikin Musulman mu, alhali kuma ba kowa bane zai yarda, ya kuma amince da hakan..
Kowa yasan Muslunci guda daya ne, kuma Allah daya muke bautawa, mun yarda da
Annabawansa,
Littatafansa,
Mala'ikunsa,
Da kuma ranar karshe.
Kar ka manta Annabi (S.A.W) yace; "Al'umma ta bazasu gushe ba sai har sun rabu gida gida har sau 73, kuma a cikin qungiyoyin nan 73, Guda DAYA (1) ce kawai zata shiga Aljannah".
Toh fa, yanzu gida nawa musulman duniya muka rabu, ina ruwanka da kafurta wani, kaima kayi ta kanka mana?
*Darika
*Tijjaniyya
*Izala
*Ahlul Sunnah
*Qur'aniyya
*Shi'a
*Haqiqa
DA SAURANSU.
Ya yan uwa musulmai, mu tuna mana lokacin da Annabi (S.A.W) yazo yin wafati, sai sahabbai suka tambaye shi, me zaka bar mana? Sai ya amsa cewa "Na bar muku Qur'ani da Hadith"
To indai kai ka tsaya akan Qur'ani da Hadith, menene damuwar ka?
Wallahi Tallahi, duk Wanda ya rike Qur'ani da Hadith, yake aiki dashi, bazai taba tabewa ba duniya da Lahira.
ABIN LURA... 2
Na rantse da Allah, ni Muhammad Auwal, kafurai ne suke zuwa suke koyon Karanta Alqur'ani, suke koyon karanta Hadisai, suke karanta Tarihi na manya-manyan malamai da annabawa, domin CIMMA BURINSU AKAN RIKITAR DA MUSULMAI.
"Allah shi kadai ne mai shiryarwa, idan ya shiryar da kai ka shiryu har abada, Idan kuwa ya batar da kai ta tabe har abada, babu mai iya shiryar da kai"
A zahirin gaskiya, kafurai da dama suna hakane dan su RIKITAR da Musulmai ta hanya daban-daban. Duk wanda kaga yana maganar batanci ga Annabi ko Allah, to kada kayi tsammani musulmi ne, a'a kawai ka dauke shi a matsayin KAFURI.
Munyi bincike sosai, mun gano haka tun a baya, suna zama a matsayin malamai, sannan suna kalaman batanci ne ga Annabi kaga duk abunda suka fada, Almajiransu zasu bisu shkenan kawunan musulmi ya rabu.
Mu dai abunda muke bukata kawai, HADIN KAN MUSULMI, kada kace kai da Darika ne, Tijjaniyya, Shi'a ko Izala.
Idan wani ya tambayeka, kai dan menene, kace masa kai DAN MUSULMI NE.