Majalisar wakilan Najeriya ta amince da wani kuduri na yin kira ga gwamnatin kasar da ta sauyawa dubban 'yan gudun hijirar da ke fakewa a makarantun birnin Maiduguri matsuguni, domin bai wa dalibai damar ci gaba da karatu.
Majalisar ta ce ana tauyewa dubun dubatar yara 'yan makaranta damarsu ta samun ilmi a birnin, saboda yadda makarantun nasu ke ci gaba da kasancewa matsugunai ga wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
Hon. Garba Chede Hammanjulde ya shaidawa manema labarai cewa 'muna son a yi musu sansani wanda za su tsuguna, kafin a samar musu wajen da za su zauna na dindindin'.
Rikicin Boko Haram dai ya raba mutane fiye da miliyan daya da gidajensu.