Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaron kasar su kara matsa-kaimi wajen murkushe masu satar fasaha a harkar fina-finai da rubuce-rubuce a kasar.
Ya yi gargadin cewa idan ba a gagguta daukan mataki ba, matsalar satar fasaha za ta yi mummunar illa ga harkar Fina-finai da aka fi sani da Nollywood a kudancin kasar, yayin da Kannywood ta fi shahara a arewacin Nigeria.
Buhari ya ce "Ana samun nasara a Nollywood. Ya kamata mu taimaka musu saboda kada masu satar fasaha su durkusar da su."
Kazalika fina-finan sun shahara a nahiyar Afirka.
Kusan fina-finai hamsin ne suke yi a kowane mako, sai dai ribar da suke ci ba ta taka-kara ta karya ba saboda matsalar satar fasaha.