UUmmi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu
hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata tafiya a hankali.daga
can gefe ta hango wata yarinya wadda bazata wuce
sa'arta ba.
tace,"yauwa,ga firdausin data tsokane ni" ta nufi
wurinta ,tasha gabanta ta rike kugu.
"fiddausi wa kike tsokana? fiddausi tace "ban tsokane ki ba fa".cikin tsoro tayi
maganar .ummi ta shako mata wuya.
ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga.ban ce ba inji
fiddausi .ummi ta hankada ta tare da cewa "Allah yaso
ki."
nikan garin da fiddausin tayi ya tarwatse a kasa tace "kin gani ko? wallahi sai kin biyani"ta soma
kuka,ummi ta sheka da gudu,sai gida.
tana ajiye man gyadan data siyo ta nufi ba daki don
fitsari ya matse ta .umma dake zaune tana fadin. "da
mutum!da mutum!!" saida ummi ta bude .
Ganin yaya Abba tayi,da gudu ta juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi bol da dakakken yajin da
umma ta daka zata soya mai don cin abincin rana. sai
kuma ta tuna cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai
binciko ta.ta fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa.
tsohuwar tana sallar azahar.ummi ta tsallake ta ta
kutsa kasan gado.nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson sha da zarar ta idar da sallah. Alhaji
babba tasa ya aiko mata da furar daga kasuwa.don
tasha da rana. Abba ya fito wanka ranshi a bace.dakin
umma ya nufa yana fadin "ummi ke ummi zonan" Ya
samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta zubar, tana
fada. Ya ce, "Umma ban san irin dukan da zan wa Ummi ba yau. Ta ce,"Abba ka mata dukan mutuwa,
na gaji da halin Ummi. Yarinya sai ka ce 'yar fata? Ka
dubata ta tafi dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a
dake ta." Ya ce,"Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta,
amma ba zan barta ba. Ya juya zai tafi, suka ji muryar
Tsohuwa tana fadin. Ba zan yi fada ba, ka kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka barta da rai. Ta dubi
Umma" ke kuma Suwaiba dama kin san ba za ki
daraja sunana ba ki ka sa a ka sa miki don kiji dadin ci
min fuska?" Umma ta ce," Ba haka ba ne Tsohuwa,
Ummi ba ta yo halinki ba. Ita fa rashin hankali ne da
ita. Yayanta fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta zubar min da barkono. Abba ya ce, "Umma
don Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta
6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta hana
a yi mata fada. Uhm duk fadanki yau sai na dake ta,
ba sunan ki ba in ma kece,"Tsohuwa tasa kuka gami
da salati. "Yanzu mai sunan Malam ni ka ke fadawa haka?" ya ce, "An fada miki." Umma ta ce, "kai Abba
zan sa6a maka jeka." Ta juyo wurin Tsohuwa, Don
Allah kiyi hakuri............... Maman Fiddausi ce tayi
sallama tare da Fiddausin suka shigo. Ran Maman
Fiddausin a 6ace, ta tsaya rike da gari a hannunta ta
dubi Umma. Ta ce, Umman Abba dubi abn da Umminki tayi min don Allah, yarinyar nan tayo nika da kyar,"
tun safe sai yanzu na samu, amma ta zubar min."
Abba ya ce, Kinga halinta ko?" Tsohuwa ta ce,
"Wannan ba matar Bala ba ce?" Maman Fiddausi ta ce,
"Ni ce." Ta ce," To kije kije ki nemi wanda ya zubar da
garinki, Ummi ko fita ba tayi ba. Umma ta ce, " Ta fita Tsohuwa, na aike ta siyan mai." Tsohuwa ta ce,"
Tsokanarta a ka yi to. Umma ta amshe abin garin ta
zuba musu, sannan ta ce, "Don Allah Tine kiyi hkr."
Abba ya nufi daki. Sai da ya shirya tsaf, sannan ya
dauki belt ya nufi cikin gida, dakin Tsohuwa ya shiga
kai-tsaye kasan gado ya nufa. Ya jawo ta, ta soma kurma ihu. Daya ya lafta mata amma ta dane shi tare
da cukwikuye belt din tana ihu. Tsohuwa ta iso tana
dukanshi a baya, fadi take "Za ka kasheta ne? Jama"a
kuyo dauki. Haushin hakan yasa shi damko kanta ya
shiga zuba mata kola, ya sirmiyota ya shiga lafta da
takalminshi, tunda ta hana belt din. Sai da ya mata tas, sannan ya fita ya bar su, Tsohuwa na kuka Ummi na
kuka. , Sai da komai ya natsa ta leka ta jawo furarta
don tasha, sai ta ganta a zube. Ta ce, A" a ke ki ka
zubar min da fura?" Ummi ta ce, To ba shi ne janyo ni
ba Yaa Abban. Tsohuwa ta ce, "Ai ko sai ya siyo min
furata. Ta mike ta wuce Umma tana rabon abinci, ta nufi soro in da dakin Abba yake (Zaure) Ya fito yana
rufe kofa, ta ce "Au za ka fita ba? To ka sawo min
furata da ka zubar. Ko kallonta bai yi ba ya rufe
kofarshi ya wuce. Ta ce mishi "Aikin bana, in ba siyo
min ba ubanka ai ya dawo ko min dare ya sito min.
Abba ya ce, Ku ku ka sani. Ra ce, kaima ka sani, dan jakar uba. Ta dawo ciki tana mitar ya cika bakin rai.
Umma ta ce, "Ina Abban? Tsohuwa ta ce, "Ya tafi, in
bai sai min furata ba ranshi zai 6aci yau a gidannan.
Umma ta ce "Ni bai ma ci abinci ba ya fita, ke Ummi zo
ki kira min shi, yunwa fa yake ji. Tsohuwa ta ce, "Ba za
ta kira shi ba, ya dake ta sannan ta kira shi? Tunda bai barta taci da dadin rai ba, shi ma ba ya ci ba.,, Umma
tayi shiry,sai haushin Ummi da take ji kamar ta shake
ta ta mutu. Ummi tayi wanka ta zura kayan Mkrnt,
tana saka sandal Umma ta ce, "Ina Ummi? Zo nan."
Ummi ta tafi tana cewa a ranta. "ALLAH YASA DAKIN
YAYA ABBA ZA TA AIKE NI, SAI NA RAMA DUKAN DA YA YI MIN JIYA, DON YANZUN DUK ME YA MIN SAI NA
RAMA.........."
Umma ta katse mata tunani da cewa,"dauki shayin
Abba ki kai masa kada yayi latti,kai shayin ki dawo ki
dauki dankalin,yau shi kadai ma nayiwa dankalin."
Tace,"nifa?"umma tace "ke kina cin dumame Abba ko ba ya ci,dan haka dan wanda ya rage shi nayi wa."
Ummi ta figi kayan tea din ta nufi dakin Abba tana
tura baki.tare da sallama bata jira amsa ba,ta daga
labule ta fada. Dabi'ar da yake mata fada akai
kullum,ya gama saka singiletinshi kenan yana kokarin
saka riga. Yace, "wai ke wace irin majanuniya ce?ban ce miki in kinyi sallama sallama sai na amsa za ki shigo
ba? sai kawai ta saki tiren,ruwan zafin ya zube masa a
kafa,dankalin ya watse kan rigar da zai saka. tayo
waje da gudu,sai dakin tsohuwa.ya fito da sauri yana
cewa,"umma ta kona ni! ta kona ni!!" da sauri umma
ta fito daga dakin Alhaji babba,shima Alhajin na biye da ita yana fadin "wacece ta kona ka?" Yace "ummi
ce! ummi ce!!."nan take Alhaji babba ya rike kafar
yana tofa mishi addu'a. Umma ta debo kullun kamu ta
zuba mishi,amma duk da haka sai da yan yatsun
kafarsa suka kumbura. tsohuwa ta fito daga daki tana
fadin,"kai ummi bata ji? wai ni meyasa aka sa mata sunana?" Abba ya kalli tsohuwa cikin takaici
yace,"duk ba ke kike daure mata gindi ba?" Umma ta
shiga dakin tsohuwa ta janye kayan da tsohuwa ta
jera don kada aga ummi,ta janyota tun daga dakin
take kwallo da ummi har waje. Alhaji ma yau har
dashi aka zane ummi,tsohuwa dai sai yan mitoci take yi,wai yanxu haka ma bata sani bane. Abba dai ranar
dai bai je makaranta ba,haka nan da yamma sai da ya
saka ummi a dakinshi ya bata gwale-gwale sannan ya
zane ta. misalin hudu da rabi na yamma,Ahmad
abokin Abba yayi sallama a kofar gidan,Abba ya amsa
ya fito. Suna zaune kan dakalin kofar gidan suna hira,sai ga ummi ta yanko da gudu tana waiwayen
baya.
Ya ce,"zo nan."tazo yace,"kinyo tsokanar fada ko?"
tace,"a'a.yace in har tsokana ki kayo zaki sani shegiya
mummuna kazama. Ta murguda baki,yasa takalmi ya
jefeta,ta shige gida sai ko ga wani yaro jiki duk kwata yayyanshi na biye dashi. ya tambayesu,suka ce "ummi
ce ta jefa shi kwata"ya taso yaron har cikin gida ya
kamota dakin tsohuwa ya tsareta ta wanke ma yaron
jiki,ta kuma wanke kayan. sannan ya zuzzuba mata
kola a kai.tsohuwa tana ta yiwa yaran fada,wai ita ma
su daina tsokanarta Umma ko lekowa bata yi ba,ya fito ya samu Ahmad yana cewa "kayi hakuri na barka
kai kadai." Ahmad yace,"ba komai" sai Abba ya zauna
sannan Ahmad ya dube shi. Abba wannan kanwar
taka kuwa bata da Aljanu? Abba yace,"ba kowa
akanta,sai iskanci." Ahmad yace."a'a,kai dai ku kaita
ayi mata rukiyya." Abba yayi dariya,sannan yace kasan Allah ba kowa akan ummi,saboda Alhaji karami
ya taba yin wannan tunanin. ya dauke ta yakai ta
rukiya bata da komai."Ahmad yace tabdi!,gaskiya in
ta isa aure duk wanda ya aureta akwai aiki babba a
tare dashi. Abba ya ce,"wane mahaukaci ne ma zaya
dibar ma kansa ummi?"Ahmad ya ce,"sai ai muku hadin ggida..." ya kaima Ahmad naushi a gefen
ciki,Ahmad ya kauce yana masa dariya. Abba ya
ce,"ka cuce ni,ace in auri ummi ai sai na hada kayana
na bar garin nan. nan. Ahmad ya s heke da dariya har da
rike ciki.sannan ya ce,"don me? Abba ya ce,"to
wannan yarinyar ba sai ta hada maka gobara gida ba?gata kazama ga muni." Ahmad ya ce,"kama dai
kuke yi." Abba ya bata rai,"Ahmad bana so.in har da
gaske ina kamada ummi ba sai na koma ciki an sake
haifana ba.
Don Allah ni tashi ma ka tafi,don wallahi da don kai
bane kake fada min haka da sai munyi rigima,na tsani ummi,bana sonta sam! Zaune suke a kofar gidan Alhaji
babba kan katuwar tabarma,sun jere abinci suna ci.
kullum Alhaji babba da Alhaji karami nan suke zama
tamkar tagwaye,suna matukar kama. mafi yawancin
lokuta ma kaya iri daya suke sakawa,domin Alhaji
babba duk kayan daya saya tare yake sai musu. haka nan hula ko takalmi,haka nan matansu baya
bambantawa.shima Alhaji karami duk da bai kai
samun babba ba yana koyi dashi. Alhaji babba ya kalli
karami yace,"Aminu ya zancen makarantar bashir?"
Alhaji karami ya dubi wansa ya ce,"Alhaji bashi fa ya
fadi jarabawa,jiya na tsare shi da maganar sakamakon jarabawarshi yace bai duba ba,saida yaji
nace zan hada shi da Abba suje sannan yace min yaje
wai duk ya fadi. Alhaji babba yace,"Ash sha! sai ya
maimata shekara kenan?"Alhaji karami ya ce,"to in
ma ba zai maimaita ba Alhaji shi ya sani,ba sahura ta
bata su ba? shi Abba ai ba haka yayi ba,ka dubi fa yadda yaki aikin kanikancin nan,uwarshi ta zuga shi
wai yayi karatu kadai yayi aikin gwamnati. kullum
haka sahura take kitsa ma yaran."Alhaji babba yayi
yar dariyar takaici,sannan yace"in banda abin sahura
yadda kasan nan tamu ta zama waye zaici alwashin
aikin gwamnati? ina ce masu digree ne ke yawo ba aiki?" "har masu masters." inji Alhaji karami.ya tashi
zaune daga kishingidar da yayi,yace dubi misalin dan
abokinnan naka Alhaji buhari."
Alhaji babba ya ce,"kwarai kuwa,mas'ud ba.yanxu
ma fa kasuwa yake zuwa,sai yanxun yake koyon
kasuwancin." Alhaji karami ya ce,"to daya dora shi a kasuwar fa tun farko?shi yasa na fada ma sahura ta
bar yara su hada da sana'ar hannu. Donni dai yaro
kamar bashir yanxun ba zan dauki kudina in ba shi
ba."Alhaji babba yace,"shi yasa kulum nake kara son
Abba,yaron nan da kanshi yace min in kai shi shagon
dinki. Har naki suwaiba ta ce,"Alhaji ka kai shi in ya iya sana'ar hannu ko bai samu aikin gwamnati ba zai
rike kanshi da sana'ar nan." Alhaji karami ya ce,"to ai
kasan ita suwaiba tasan abinda take yi.amma sahura
sai addu'a." Sallamar Abba ce ta katse su,ya zauna can
gefe sannan ya gaishe su,duk suka amsa tare da tara
hankulasu gurinshi. Ya mika ma Alhaji babba kullin takarda tare da cewa
"Alhaji gashi maganin (ulser)ne" Alhaji babba ya amsa
ya ce,"Abba sarkin amsa magani, a gurin wa ka samo
wannan kuma?" ya ce,"Ahmad abokina na raka ya
amso ma babanshi,shine nace bari in amso muku"
yace to Allah ya saka da alkairi."Alhajikarami yace"dame ake sha?" Abba ya ce,"da madara peak."
suka ce"to" daya mike zai shiga gida Alhaji babba
yace ya shige da kwanikan abincin. yau kam Abba
bacci yake ji da wuri,don haka ya baro shagon
dinkinsu wanda ya kan kai goman dare a ciki ya nufo
gida. Ya bude dakinshi ya shiga ya cire riga sai singileti da gajeren wando na jeans.ya nufi ciki don ya kama
ruwa ya kuma yi wa ummanshi sallama. tsakar gida
ya sameta zaune ta zabga tagumi,inda abinda Abba
ya tsana shine,yaga ummanshi cikin damuwa. da sauri
ya isa wurinta,"umma lafiya?"ta dube shi "ina fa
lafiya,ummi ce tunda tayi sallar isha'i ta fice kusan awa guda zance jiya ka mata dukan fita wasan dare?"
Abba yace "to wai me za'a yi wa ummi ne ta zama
irin sauran yara?" umma tace,"addu'a ce Abba,kuma
muna yi kullum." ya juya cikin bacin rai,layin su Amina
kawarta ya nufa,don bata wuce can.duk da cewa
Amina bata kaita rashin ji ba. can din kuwa ya sameta,ta tara zugan yayan layi sai tsokanar fada
suke yi,ita ce shugaba. wata falwaya Abba ya samu
ya jingina yana kallonsu,don yana iya tunkararta su
diba da gudu. shi kam ba za ya iya guje-gujen nan
ba,duk wanda yazo wucewa sai sun tsokane shi,wani
su jefe shi,wani kasa zasu watsa masa su gudu wani kuma rigarsa zasu ja. c can wani shida budurwarsa sun
zo
wucewa ta fizge ledar hannunsu ta watsar,sannan
suka ruga da gudu. tayo gurin da Abba ke tsaye bata
zaci da mutum a gurin ba,sai dai taji anyi caraf da
ita.sai da Abba ya zabga mata koso a tsakiyar kai har tayi fitsarin wuya,sannan ya tasata har gurin mutumin
data yaga ma ledar. suna tsugunne suna tsintar
lemunsu da ayaba ya ce,"malam ga wadda ta yaga
muku leda." da zafin nama mutumin ya mike,Abba ya
ce,"gata"mutumin ya shakota yace yau sai naga
ubanki." Abba ya ce,"ko kara ka kai gidansu nine zan hukuntata,don haka gata na kawo maka kanwata ce
kuma naga lokacin data tsokaneka." jikin mutumin
yayi sanyi ya ce,"na gode bawan Allah,taje taci
albarkacinka." Abba yace "daka nade ta." mutumin
yace,"ba komai,ke kuma ki canza hali ke mace ce."
Abba yace nagode" sannan ya tasa ta zuwa gida. Bokiti ya cika da ruwa ya dora mata,,umma rasa
bakin magana tayi daya sanar da ita tsokanar daya
tarar da ummi suna yi. Daga karshe ta ce,"Allah ya
shiryaki,abind ya sameki kada ya sami sauran dangi.
Alhaji kuwa daya sameta dauke da bokitin tana kuka
tana fadin "yaya Abba na tuba,bazan sake ba." ya ce,"uwata bakya ji ne fatan Allah yashirye ki."ya nufi
dakinshi.tsohuwa takaicin Abba ne ya hanata fitowa
tayi magana. nata ganin,ummi bata wuce fita tayi
wasa da kawayenta ba,a cewarta ba laifi ba ne.
amma an bi an tsangwami yarinya,an hanata
walawa.sai da Abba ya gaji dan kanshi sannan ya sauke mata ruwan.
Sannan ya mammaka mata takalmi,sannan ta shige
dakin tsohuwa.tsohuwana daga kwance ta dubeta.
"yaga dama ya kyaleki?kai mai sunan malam akwai
mugunta.zo ki kwanta." cikin kuka ummi
tace,"kayana sun jike,bokitin ruwa fa ya dora min."tsohuwa tace,"barshi da halinsa,ace mutum ba
zai sake ba?" ummi tace,"ai sai na rama,shima din sai
yayi kuka."tsohuwa ta ce,"a'a,kada ki soma zancen
ramakon nan.kin san ko kin rama ke ce zaki kwan
ciki." ummi ta ce,nifa sai na rama."tsohuwa ta ce,"baki
gaji da shan wahala ba kema da shegiyar gaddama,ga zanina nan kikin raki ciro ki daura kizo ki kwanta."
ummi tayi lamo bayan tsohuwa tana tunanin dame
zata rama abinda Abba yayi mata jiya.har bacci yayi
gaba da ita waiwaye............. SULAIMAN shine asalin
sunan Alhaji babba,Aminu kuma shine Alhaji karami.
tsohuwa itace mahaifiyar su,kuma su kadai ne yayan data haifa.Asalinsu yan zamfara ne a kauyen daji a
karamar hukumar kauran-namoda. malam Idris
mahaifinsu shine ke zuwa yawon fatauci,har Allah ya
zaunar dashi a garin kano,da matarshi Habiba. sunzo
da yayansu guda biyu,sulaiman da Aminu.sun yi
karatun muhammadiyya mai zurfi,amma basuyi karatun boko ba. sannan ya dora sukan harkar
kasuwanci,Allahya albarkaci kasuwancin Sulaiman
inda harkoki suka bude mishi cikin kankanin lokaci.
matsalar shi daya rashin boko,malam idrisu
mahaifinsu yana daya daga cikin wadanda basu amshi
boko ba lokacin da tazo. Don haka sam bai saka yayansa ba.Sulaiman ya auri Suwaiba wadda suka
dauki watanni suna soyayya,ita yar unguwar sheka
makaranta ce. Amma asalinsu yan Daura ne jihar
Katsina.kafin aurensu sai da yayi gini a unguwa uku
gidaje guda biyu iri daya. Ya ce Aminu kaninsa ya zabi
gida duk da cewa a lokacin baiyi auren ba,wannan abu yayi wa mahaifisu dadi. yayi ta shiwa Sulaiman
albarka,don haka sai aka rufe na Aminu,yayin da
sulaiman ya tare a nasa da matarsa Suwaiba.