A 'yan kwanakin nan, kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya a arewacin Najeriya na ta kai hare-hare a yankin, inda a daren jiya ma rahotanni ke cewa sun kai wani hari a garin Ngalda da ke jahar Yobe.
Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun shiga garin Ngalda da ke jahar Yobe a daren jiya, inda suka yi awun gaba da kayan abinci da dama da kuma wasu ababan hawa.
Sai dai bayanan da ke fitowa daga yankin na nuni da cewa babu wanda ya jikkata daga harin.
“Sun shigo sun debi abinci da kuma babura guda biyu, abin da na gani ke nan.” Inji wani mazaunin garin wanda ya tattauna da Muryar Amurka ta wayar talho amma ya nemi kada a ambaci sunansa.
A cewar wadanda suka shaida lamarin, a lokacin da suka shiga garin duk sai mutane suka arce cikin jeji wasu suka buya akan bishiyoyi.
“Mun gudu jeji mun hau bishiya, da suka tashi fita sai suka kashe fitilun motocinsu amma ana hangen danjar motocinsu, sai suka yi wajen Sheka.” Mutumin ya kara da cewa.
Bayanai sun kari nuni da cewa maharan sun isa garin ne a cikin motoci guda biyu da ba a tantance kirarsu ba da kuma babura guda biyu sannan babu wanda ya san adadinsu.
Babu wanda dai ya jikkata a wannan hari, yayin da rahotanni ke cewa wasu jami’an tsaro sun isa garin bayan wannan ficewar maharan.
A halin yanzu da ake ciki, wasu mazauna garin sun koma yayin da wasu su ka ci gaba da kauracewa garin na Ngalda saboda rashin tabbacin lamarin.
Title :
Yobe: Boko Haram Ta Kai Hari a Ngalda
Description : A 'yan kwanakin nan, kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya a arewacin Najeriya na ta kai hare-hare a yankin, inda a daren jiya ma rah...
Rating :
5