Bayan Jameela ta samu Addmssinon a A.B.U,mussadik yayi mata murna kamarshi yasamu.Lokacin tafiyarta yayi tun saura sati guda take kukan rabuwa da masoyi,shiko Mussadik kullum maganarsa bata wuce"kirike alkawari,ita kuma sai tace ai ita aduniya babu wani da namiji da zataso kamarshi,hakan yana samai natsuwar zuciya,amma idan ya tuna cewa,Jami'a zata,kuma gurine mai mutane iri iri ga ban bancin yare addini da rayuwa,sai hankalinsa ya kara tashi,gaskiya daso samune da tare mukatafi,ya fada azuciyarsa,yace to amma Allah shi yasan dalilin hakan. Ranar da Jameela zata tafine,ta kawomin hotunanta har guda goma,gaskiya nayi farin ciki,duk da cewa mun rabu muna kuka,bazan manta da ranar nan ba domin itace ranar farko da muka fara nesa da juna.Muka tsaya a bayan gidanmu kukan tsintsayene kawai suke tashi,munkasa cewa da juna komai mun kurawa juna ido kowa kwalla ta cika idonsa. Nasa hannuna na share hawayenta,na dafa kafadunta da hannayena,nace"to princessess Meela kisani,zan shiga maraici,narashinki kusa gareni,sanin kankine cewa bana iya rabin awa batare da nagankiba,yau gashi takai ga har zan iya kwanaki ban gankiba,ya fashe da kuka.Jameela ta fashe da kuka tace"kasani Mussa kaine jinin dake kewayawa cikin jikina,kuma kaine ruhina,konaje can gangarjikina kawai zasu gani amma ruhina da zuciyata suna tare dakai a koda yaushe. Sukaci kuka har suka gaji suka zauna kowa ya tankwashe kafa suna kallonjuna,Mussadik ya sunkuyar da kansa kasa yace"Meela wlh hankalina a tashe yake,domin nasan campus akwai manyan yara,kullum mafarkina da fatana kizamo tawa amma ina tsoro kar su kwaceminke.Ta dago kai tace"wato baka yarda daniba ko?to ai inda maza ke bina kaima haka mata suke binka.Yayi mur mushi yace"na yar da dake dari bisa dari,amma kisani ina ganin kamar force din attraction dinmu zai ragu ne.Ta dago kai tace"ai duk duniya babu force din dayafi naso karfi,baruwansa da nisa ko kusa mutukar masoyan sun rikewa juna alkawari,agunka naji wannan maganas,amma yanzu kake fadin haka?Yace nasan da wannan fatana murikewa juna alkawari,sukai alkawari babu zancen rabuwa sai dai mutuwa,kuma ba wanda zai so wani ko wata a tsakaninsu sai junansu. Jameela taje lactuer ta dawo,babu abin da take tunani aranta sai mussadik,tana kwanciya kan katifar ta ta tura kiran waya,yana duba sreen yaga sunanta dara dara PRINCESSESS MEELA sai yayi ajiyar zuciya ya dauka,yayi sallama,ta amsa yace"tunda safe nake kiran wayarki amma akashe,tace E wlh naje lactuer ne.yakake mussana?yace ba lafiyaba hankalinta ya tashi tace"meya sameka?ciwon rashinki ne yasameni.sai ta sheke da dariya tace wlh har ka tsoratani,kayi hakuri kaji baby na,zan kasance tare da kai ko da yaushe a waya.Yayi murmushi yace"bakomai kunne da baki su zasu samu nasu amma idona ya dauki azumin rashin ganinki,tace niko kaga ina ganinka da idanun zuciyata,nasan yanzu kana zaune,a kofar gida gurin da muke zama.Yace haka ina nan a gurin gani nake kamar zaki futo naganki wayyo masoyiyata Meela.Tace kayi hakuri,mai kaunata,karka damu kanka ni mallakinkace. Tafiya tai tafiya,kullum sai sun wuni waya,kuma dare nayi zasuyi ta free call.so yayya kamar sa hadiye juna. Bayan zangon karatu ya kare,tun dasuka fara jarabawa take kirga kwanakin da zata koma gida dan gann masoyinta,shiko Mussadik zana kwanakin yayi a dakinsa kullum yatashi sai ya soke kwana daya harzuwa ranar karshe,tana gama jarabawarta,tazo tai wanka tashirya,kawayanta suna bazaki tsaya ki dan hutaba,tace ina sai gida.suna mota yana tambayarta kunzo ina tace munzo tashar yari,bayan kamar rabin awa yakuma bugowa,tace suna kwannar dangora,kamar rabin awa sai gata a kofar gida a dai daita. Tana sauka suka kure juna da kallo,hawaye kawai ke zuba daga ida nuwansu,mai adai faita yace"kai kudina?Mussadik ya zaro dari biyar ko dubawa baiyiba yamika mai,mai adai daita yace"malam nifa bani da canji,Mussadik kallonta kawai yake kokulashi baiyiba,yakuma mai maitawa nifa bani da canji,Mussadik yace jeka,yace kabarmin canjin?yace e. Ya kama jakarta yana ja suka karasa kofar gida,yace"oh my Princessess haka kika kara kyau?Tayi mai wani kallo ta lumshe ido tace"um my prince,kaine ka kara kyau gashi naga kamar ka kara tsawo,da jiki,ji damtsenka yadda ya kara girma,baka dena zuwa daga karfen dana hanakaba ko?hm na denamana kawai dai kwallo nake zuwa,nasan ai ita bazaka iya denawaba.suka tsaya kamar minti goma kallon juna kawai suke,tace bari naje nai wanka nai maka kwalliya na futo.yace to,tana shiga gida yayi wani tsalle yace"yes thats my Princessess. Kamar awa daya darabi ya shiga gida yasake buga wanka ya sako kaya harda p cap,tana futowa ta dubeshi tace"hm my prince u look gogeous"ya kalleta bai ma san me take cewaba domin tarudashi kamar yadda shima ya rudata,suka zauna sukai wani ta gumi da hannu kowa na kallon kowa. Yadan numfasa yace"my princessess ya karatu?ta harareshi tace"baka cemin ya rashinkaba sai ya karatu?yace sowy to ya rashin mu ga juna?tai murmushi tace gaskiya munsha wuya,amma nafika shanwuya.Ya harareta yace um