Wadanda ake zargin mayakan Boko Haram ne sun harbe mutane a kalla arba'in a wasu kauyuka biyu da ke jihar Borno a Nigeria.
Mazauna kauyukan Debiro Hawul da Debiro Biu a karamar hukumar Biu, sun bayyana cewar 'yan Boko Haram sun je kauyukan ne a kan babura da akori-kura sannan suka kama harbi ba kakkautawa tare da kuma kona gidaje da kwashe kayayyakin jama'a.
Haka kuma an kai hari a kauyen Yebbi da ke yankin Bosso a Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Nigeria inda aka kashe mutane kusan biyar.
A ranar Talata ma wata 'yar kunar-bakin-wake ta hallaka mutane kusan 10 tare da raunata wasu da dama a kasuwar Gujba da ke jihar Yobe.
Sannan kuma a ranar Litinin, wasu mata 'yan kunar-baki-wake suka tayar da wani bam a kasuwar tashar Baga da ke Maiduguri inda mutane fiye da 20 suka rasu.
Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kaddamar da hare-hare a yankin arewa maso gabashin kasar tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kujerar mulki inda ya yi alkawarin murkushe ayyukan masu ta da kayar baya.
Title :
Yan Boko Haram sun Halaka Mutane 42 A Biu
Description : Wadanda ake zargin mayakan Boko Haram ne sun harbe mutane a kalla arba'in a wasu kauyuka biyu da ke jihar Borno a Nigeria. Mazauna kauy...
Rating :
5