A ranar 5 ga Agustan bara ne mayakan Boko Haram suka suka kwace garin Gwoza da ke Jihar Borno tare da ayyana garin a matsayin hedkwatar Daular Musulunci a Afirka ta Yamma a karkashin jagorancin Abubakar Shekau. A lokacin da mayakan Boko Haram din suka kwace garin sun kone wani bangare na fadar Sarkin Gwoza lamarin da ya sanya suka nemi wani gida na daban don kasancewa gidan da Shekau zai zauna. Gidan Alhaji Aliyu Abacha da ke garin Gwoza ne mayakan suka zaba a karshe, kuma matarsa Malama Balaraba Aliyu Abacha ta shaida wa wakilinmu faru yadda lamarin ya faru kamar haka: Ranar Talata da 5 ga Agustan bara da yamma muna zaune lafiya, kwatsam, sai ’yan Boko Haram a karkashin jagorancin shugabansu Abubakar Shekau da ayarin motocinsa kimanin hamsin da wasu a kan babura suka farmaki garin Gwoza, inda jama’a suka watse suna gudun tsera da rai maza da mata. Mai gidana ya ruga da gudu ya hau katanga domin ya tsera da ransa, amma sai kaddara ta riga fata ya fadi ya karye a kafa. Wannan ya sa aka tallafa masa inda surukarsa wato mahaifiyata ta kai shi gidan surukinsa wato gidan mahaifinmu.”
Malam Balaraba ta ci gaba da cewa: “Sai ’yan sharar fage na ’yan Boko Haram din suka shigo gidanmu suka ce matan da ke gidan wato gidan Aliyu Abacha su fice domin Amir wato Shekau zai shigo gidan kuma dakin Balaraba ne aka zaba masa don ya zauna a ciki wato gidan mijina ya zamo sabon fadarsa saboda sun kone wani bangare na fadar Sarkin Gwoza a lokacin.”
Ta ce gidansu babba ne da ke dauke da kayan alatu. Kuma mayakan Boko Haram din sun ce duk wanda ya yi musu da su, za su aika da shi Lahira, ko kuma su kai shi dajin Sambisa wanda suke kira da rizab.
Balaraba ta ci gaba da cewa ba ta taba ganin Amir din ba, domin yana zaune ne a cikin mota. Kuma jeren motocin da suka yi masa rakiya sun kai motoci hamsin. Sai suka tambayi makullan motcoinsa. Ta gaya musu cewa daya na wurinsa, daya na wurin direba.
Ba su nemi kudi don fansar rai ba:
Balaraba ta ce mayakan Boko Haram ba su nemi a ba su kudi domin fansar rai ba, dalili kuwa shi ne su ran kawai suke nema su dauka, ta ce duk wanda yake namiji dan shekara 10 zuwa 13 zuwa sama, to matacce ne idan suka hadu da shi.
Ta ce bayan ta bar gidan mijin nata: “Ina isa gidan iyayena sai na sume, sai bayan kwana hudu na farfado, sai maigidana ya zo ya same ni a ranar Asabar.”
Balaraba ta ce bayan da mijinta ya karye a korar ta ’yan Boko Haram, sai ta yi niyyar fitar da shi daga garin da misalin da karfe 1:00 na dare a kurar sayar da ruwa. Amma sai maigidanta ya ce ta fitar da yara ta kai wa abokinsa, sai dai ta ce da ta fita kafin ta dawo ’yan Boko Haram sun shiga gidan iyayenta inda mutum biyu daga cikinsu suka ce a bar shi tunda ya karye, amma mutum daya ya ce a kashe shi. Ta ce har sun fita waje sai daya ya dawo ya harbe shi da bindiga a ranar 9 ga Agustan 2014 da La’asar.
“Sai mahaifiyata ta yi kuru ta nufi gidan da Amir yake wato gidan mijina da Abubakar Shekau ya mallake domin ta dauko fararen kaya don a sa masa a matsayin likkafani, amma sai ta ga abin mamaki domin sun dauke kayayyakinsa suna amfani da su. Sai suka ce me ya kawo ta, sai ta ce tana so ta shiga ta dauki fararen tufafinsa ne domin a sa masa don a yi masa jana’iza, sai suka ce in ta kara dawowa gidan za su kashe ta domin “Amir na Gwoza” ba ya son a dame shi. Wannan bayani ya sa mahaifiyata ta tara mata aka binne shi domin babu sauran maza a garin sai tsofaffi marasa gata wadanda babu wanda zai dauke su ko ya ce su taho inda yake. Mu mata kimanin ashirin muka yi masa jana’iza ba wankar gawa a gurguje ba shiri, muka yi addu’a muka yayyafa masa ruwa,” inji Balaraba.
Ta kara da cewa, saboda watsewa da garin ya yi sai suka yi amfani da wuka da ludayin karfe da fartanya suka haka kabari suka binne shi a bayan dakin mahaifiyar matarsa.
Ta ce da ta ga an kashe mijinta sai ta yi tunanin kada su tafi da ’yarsa wacce ita ce ’yar fari mai kimanin shekara 14 wato kada su yi musu abin da suka yi wa ’yan matan Chibok.
Don haka suka yi hijira suka bar garin inda suka yi tafiya a kasa tunda Asuba har sai da dare ya yi sannan suka isa garin Madagali a tsorace ba maganar neman ruwa duk da suna jin kishi da yunwa, ta ce ga gawarwaki ba iyaka a yashe a kasa. Ta ce sun yi kusa da Madagali ne sai ’yan sandan kwantar da tarzoma suka debe su a garin Dumun-Kara aka shigar da su Madagali suka yi kwana hudu.
Balaraba ta ce tana jiran ta ga mahaifiyar marigayi mijinta Aliyu Abacha da aka kashe don ta gaya mata abin da ya faru domin ba ta da labarin ta’addancin da aka yi wa danta.
Ta ce ana nan sai mahaifiyarta ta ce ’yan Boko Haram sun kore s u daga Gwoza, sun je Madagali ba su tsira ba, bayan Balaraba ta yi kwanaki uku da fita takaba sai ta je garin Geidam inda ’yan Boko Haram suka farmaki garin suka watsa su, daga nan ta nufi garin Damaturu a Unguwan Kataro inda bayan makonni uku sai ’yan Boko Haram suka kara tarwatsa su, sannan suka bi mata da ’yan mata da masu ciki suka tafi da su. Ta ce sai ta ce abin da ya fi shi ne tunda ta dan samu lafiya sai ta nufi Kaduna don can tana da ’yar uwa da za ta taimaka mata kafin su koma garinsu.
Ta ce ta nufi Maiduguri daga Kaduna saboda zaman lafiyar da ta yi da kishiyarta domin ta yi mata barkar haihuwar da ta yi a watan Disamba. Ta kuma samu damar rubuta sunanta a cikin ’yan gudun hijira.
Ta ce Haka bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zabe, ta koma Maiduguri domin ta kara rubuta sunanta don an ce gwamnatin Muhammadu Buhari da na Kashim Shettima za su taimaka musu idan an kwato garin Gwoza don su koma nan gaba.
Ta ce abin bakin ciki shi ne da ta hadu da wata makwabciyarsu a Maiduguri ta shaida mata cewa a lokacin da ’yan Boko Haram suka ji sojoji sun nufi garin na Gwoza sai suka banka wa garin wuta gaba daya, inda gidansu ya kone kurmus.
Balaraba ta ce wani karin abin bakin ciki shi ne an aiko mata cewa kishiyarta ta rasu a ranar 9 ga Mayun da ya wuce inda ta bar ’ya’ya biyar. “Yaran a yanzu suna wurin kanen mijinmu wanda matashi ne mai ’ya’ya biyu da ke zaune a garin Damboa, ga shi kuma an kara masa nauyi,” inji ta.
Balaraba ta ce ta yi wata shida ba ta da lafiya sakamakon tashin hankalin da ya so sanya ta zautuwa, sakamakon kashe mata miji wanda ta gan shi ba rai a cikin jini, kuma mata ne suka binne shi a cikin tsoro, sannan an kore su daga garinsu. “Haka ya sa ba na iya yin barci, ga hawan jini sai na sha magani nake iya runtsawa,” inji ta.
Balaraba Abacha ta ce mutuwar abokiyar zamanta a baya-bayan nan ta dame ta matuka. Domin tana tunanin yadda yaran za su kasance ganin marigayi mijinta maraya ne kuma ya mutu ya bar marayu.
A yanzu ta ce ta zuba ido ne dmion ganin yadda gwamnati za ta gyara musu garinsu da gidajensu don su koma Gwoza su ci gaba da rainon marayun da Allah Ya bar musu.
Title :
Yadda ’yan Boko Haram suka kashe mijina suka maida gidansa fadar Shekau – Balaraba Abacha
Description : A ranar 5 ga Agustan bara ne mayakan Boko Haram suka suka kwace garin Gwoza da ke Jihar Borno tare da ayyana garin a matsayin hedkwatar Daul...
Rating :
5