A Najeriya dai awoyin da ake yi a kullum da azumin watan Ramadan kafin a sha ruwa ba sa wuce sha biyar (15) ko kasa da haka.
Yawanci dai a nan Najeriya a kan iya cin abincin Sahur har kusan karfe hudu da rabi na asuba (4.30am) a garin Maiduguri ta Jahar Barno, ko kuma karfe hudu da minti hamsin na asubahi (4.50am) a birnin tarayya na Abuja.
Sannan kuma a kan fara shan ruwa tun daga karfe shida da minti arba’in (6.40pm) a Maiduguri, ko kuma karfe shida da minti hamsin (6.50pm) a Abuja.
Hakan yana nuna cewar al’ummar Musulmi a Najeriya suna yin azumin akalla awa goma sha hudu (14) ke nan a kowace rana.
To amma hakika ni da abokin tafiya ta, wato uban marayu a Jahar Barno, Barista Zannah Mustapha, mun ga abin mamaki a kasar Switzerland, saboda a kwanaki ukun da muka yi na farkon wannan wata mai albarka, sai da muka kwashe sa’o’i kusan ashirin (20) da azumi a bakinmu kafin mu sha ruwa.
Ni da Zanna Mustapha dai muna cikin mutane 29 ne da gwamnatin kasar Switzerland ta zabo daga kasashen duniya ta ba su wani gurbi na musamman na samun horo na makonni biyu a kan muhimmancin sasantawa (Peace Mediation) a kan lamurra da suka rincabe, kamar yakin basasa ko na addini ko na siyasa, da makamantansu, sannan aka kasa samo mafita ta hanyar amfani da bindiga.
Mun yi wannan taro ne a wani kauye da ake kira Oberhofen da ke gundumar Thun na Yankin babbar birnin Bern.
Haka kuma cikin dukkanin mutanen da suka halarci wannan kwas, mu uku ne kadai muke yin azumi. Na ukun namu wani Balarabe ne mai suna Almarari Masoud Bin Khalifa, wanda ya zo daga kasar Oman.
Ita dai Switzerland wata kasa ce mai arziki sosai a can yankin turai. Bacin tsananin yanayin sanyi da mutanen kasar suke fama da shi, lokutansu ma suna da matukar bambanci da namu a nan Najeriya da nahiyar Afirka da kuma sauran kasashen duniya.
Su dai a can awowin rana sun fi na dare yawa, don haka lokacin hada-hadar rayuwa ya fi na yin barci yawa. Wannan yanayi shi ne ya sa muka dandana kudarmu a kwanaki ukun farko na wannan wata mai albarka.
A daidai makon farko na wannan azumin, a kan yi sallar Asuba ne da karfe biyu da minti arba’in da hudu na dare (2:44am) a yankin da muke na kasar Switzerland maimakon karfe biyar na safe (5.am) a nan Najeriya. Don haka ne ya zama tilas muke yin sahur da misalin karfe biyu na dare. Rana kuma takan fito ne zuku-zuku da misalin karfe biyar da minti talatin da shida (5.36am).
Babban abin mamaki kuma shi ne, rana tana faduwa ne da misalin karfe tara da minti ashirin da takwas na dare (9.58pm). Don haka mukan sha ruwa ne da misalin karfe tara da rabi na dare (9.30pm).
Sallar Isha’i kuma sai karfe goma sha biyu na dare (12.03am) ake yinta.
Wannan yanayi yana nuna cewa mai yin azumi a Switzerland yana da damar cin abinci ne na misalin awowi hudu da rabi kawai.
Tsakanin sallar Azahar da la’asar ma akwai tazara sosai, domin akan yi sallar azahar ne da misalin karfe daya da minti talatin da biyar na rana (1.35pm). Amma kuma sallar la’asar sai karfe biyar da minti arba’in da biyar (5.45pm) ake yin ta, wato tsakaninsu akwai kusan awowi biyar.
Wannan yanayi ne ya sa tilas muka canja tsarin cin abincinmu, musamman ganin cewa sauran abokanan karatunmu akan dafa musu nasu ne sau uku a otal (hotel) din da aka ajiye mu.
Mun shiga wani yanayi na alhani domin babu abubuwan da muka saba shan ruwa da su a nan gida, kamar kunun tsamiya da kosai da tuwo da sauransu.
Sai dai kuma babban abin al’ajabi shi ne yadda hukumar harkokin kasasan waje ta kasar Switzerland din ta umarci ma’aikatanta da suke tare da mu a wajen kwas din da su tabbata sun yi mana dukkanin abubuwan da muke bukata na yin azumi.
Don haka ne tun wajan kwanaki uku kafin watan ya tsaya suka kawo mana wadansu takardu muka cika, inda muka bayyana musu irin abincin da muke bukata, kamar dabino da shayi da shinkafa da kayan marmari.
Hakan kuwa aka yi, domin a ‘yan kwanakin da muka yi, ma’aikatan otal din sukan shirya mana kayan buda-baki da misalin karfe tara da rabi na dare, sannan kuma su kawo mana kayan yin sahur da m isalin karfe biyu na dare. Rana kuma takan fito ne zuku-zuku da misalin karfe biyar da minti talatin da shida (5.36am).
Babban abin mamaki kuma shi ne, rana tana faduwa ne da misalin karfe tara da minti ashirin da takwas na dare (9.58pm). Don haka mukan sha ruwa ne da misalin karfe tara da rabi na dare (9.30pm).
Sallar Isha’i kuma sai karfe goma sha biyu na dare (12.03am) ake yinta.
Wannan yanayi yana nuna cewa mai yin azumi a Switzerland yana da damar cin abinci ne na misalin awowi hudu da rabi kawai.
Tsakanin sallar Azahar da la’asar ma akwai tazara sosai, domin akan yi sallar azahar ne da misalin karfe daya da minti talatin da biyar na rana (1.35pm). Amma kuma sallar la’asar sai karfe biyar da minti arba’in da biyar (5.45pm) ake yin ta, wato tsakaninsu akwai kusan awowi biyar.
Wannan yanayi ne ya sa tilas muka canja tsarin cin abincinmu, musamman ganin cewa sauran abokanan karatunmu akan dafa musu nasu ne sau uku a otal (hotel) din da aka ajiye mu.
Mun shiga wani yanayi na alhani domin babu abubuwan da muka saba shan ruwa da su a nan gida, kamar kunun tsamiya da kosai da tuwo da sauransu.
Sai dai kuma babban abin al’ajabi shi ne yadda hukumar harkokin kasasan waje ta kasar Switzerland din ta umarci ma’aikatanta da suke tare da mu a wajen kwas din da su tabbata sun yi mana dukkanin abubuwan da muke bukata na yin azumi.
Don haka ne tun wajan kwanaki uku kafin watan ya tsaya suka kawo mana wadansu takardu muka cika, inda muka bayyana musu irin abincin da muke bukata, kamar dabino da shayi da shinkafa da kayan marmari.
Hakan kuwa aka yi, domin a ‘yan kwanakin da muka yi, ma’aikatan otal din sukan shirya mana kayan buda-baki da misalin karfe tara da rabi na dare, sannan kuma su kawo mana kayan yin sahur da misalin karfe sha biyu da rabi na dare.
A kauyen da muka zauna dai babu Musulmi ko daya, don haka ma’aikatan otal din da muka zauna, har kuma da sauran abokan karantunmu, kamar wadanda suka zo daga kasashen Bogota da Ukraine da Djibouti da Berlin da Helsinki da Bujumbura da Philipines da Sri lanka da sauransu, sun yi matukar mamakin yadda muke iya yin sa’o’i har ashirin ba tare da mun ci abinci ba.
Amma kuma turawan da ke kula da mu, kamar su Matthias Siegfried da balerie Sticher da Corinne bon Burg sun yi matukar kokarin ganin cewa ba mu samu wata matsala ba.
Musulunci dai shi ne addini na biyu da ya fi bunkasa a kasar Switzerland bayan addinin kiristanci.
Bincikena ya nuna cewa kashi 4.9 cikin dari na mutanen kasar Musulmi ne, kuma sun fi zama a garuruwa kamar su, Basel-Stadt da Glarus da St. Gallen da Thurgau da Schaffhausen da Aargau da Solothurn da Zürich.
Haka kuma kusan kashi 88.3 cikin dari na musulmin ‘yan asalin kasashen waje ne da suka fito daga kasashen Bosniya da Albaniya da Kosobo da Turkiyya da kuma kasashen Afirka.
Babban abin farin cikina shi ne yawancin mutanen da muka hadu da su a Switzerland sun yi mamakin yadda musulmi suke da dauriyar yunwa, musamman ganin cewa za mu iya ajiye azumin a matsayinmu na matafiya.
Da ni da Zannah Mustapha mun ba su mamaki matuka saboda mun ki cin abinci da yamma a wata rana da aka shirya mana wata liyafar cin abinci a cikin wani babban jirgin ruwa.
A halin yanzu dai mun kammala taron lafiya kuma mun dawo gida lafiya.