Kungiyar IfeanyiUbah ta yi rashin nasara a hannun Wikki Tourists har gida da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 14 da suka fafata ranar Lahadi.
Wikki ta zura kwallo a raga ta hannun Chukwudi Samuel saura minti 13 a tashi daga wasan, kuma hakan yasa ta hada maki 26 daga wasannin 14 da ta yi.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga Giwa FC ta ci El-Kanemi kwallaye 3-1, yayin da Enyimba ta doke Nasarawa United da ci 2-0 a Aba, sai Akwa da Warri Wolves da suka buga kunnen doki.
Fafatawa tsakanin Kano Pillars da Dolphins ta shi suka yi 2-2, yayin da Sharks da Heartland suka tashi wasa 1-1.
Ga sakamon wasannin mako na 14 da aka buga.
Giwa FC 3-1 El-Kanemi
FC Ifeanyiubah 0-1 Wikki
Sharks 1-1 Heartland
Enyimba 2-0 Nasarawa Utd
Bayelsa Utd 2-0 Kwara Utd
Lobi Stars 2-0 Abia Warriors
Akwa Utd 1-1 Warri Wolves
Rangers 1-0 Sunshine Stars
Kano Pillars 2-2 Dolphins
Title :
Wikki Tourists ta doke IfeanyiUbah da ci 1-0
Description : Kungiyar IfeanyiUbah ta yi rashin nasara a hannun Wikki Tourists har gida da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 14 da suka...
Rating :
5