Wani dan bindiga dadi da ya bude wuta a cikin wata majami'a a South Carolina da ke kasar Amirka.
Wani dan bindiga dadi da ya bude wuta a cikin wata majami'a a South Carolina da ke kasar Amirka ya hallaka mutane tara, yayin da wasu da dama suka samu raunika.'Yan sanda suna ci gaba da neman wannan dan bindiga da ya yi harbin, inda suka ce akwai yuwuwar harin yana da nasaba da nuna kiyayya wa bakaken fata da ke kasar ta Amirka.