Manchester United za ta yi zawarcin dan kwallon Bayern Munich, Bastian Schweinsteiger da dan wasan Real Madrid Sergio Ramos.
Kociyan United, Louis van Gaal, yana kokarin kara karfin kulob din a kakar wasanni ta badi, ganin yadda suka kare a mataki na hudu a teburin Premier bana.
Schweinsteiger, mai shekaru 30 dan kwallon Jamus da Ramos, mai shekaru 29 dan kasar Spaniya suna daga cikin 'yan wasan da kocin ke fatan kawo su Old Trafford.
Yarjejeniyar Ramos a Real Madrid za ta kare ne a shekarar 2017, yayin da kwantiragin da Bayern ta kulla da Schweinsteiger za ta cika a karshen kakar wasan 2016.
Title :
United na zawarcin Ramos da Schweinsteiger
Description : Manchester United za ta yi zawarcin dan kwallon Bayern Munich, Bastian Schweinsteiger da dan wasan Real Madrid Sergio Ramos. Kociyan United...
Rating :
5