Allah ya kawomu Watan Ramadhan, Lokacin da zaka ji Wa'azi yana fitowa ta ko ina.. Tafseeri a Masallatai, Tafseeri a Makarantu, Tafseeri a gidajen Radio da Talabijin ..
Duk wannan BIDI'A ce mai kyau.. To amma abin tambayar anan shine:
¤ SHIN MUTANE SUNA WA'AZANTUWA DA MAGANGANUN DA SUKE JI AWAJEN MALUMA KUWA??"
¤ SHIN MUTANE SUNA AIKI DA ABINDA SUKA JI ACIKIN WA'AZIN NAN KUWA??
¤ SHIN SU MALUMAN SUNA AIKI DA ABINDA SUKE KARANTARWA KUWA??
¤ SHIN SUNA TSAYAWA NE AKAN TSANTSAR GASKIYAR DA ALLAH YA FADA, KO KUWA SUNA CHUDANYAWA DA SON ZUCIYARSU??
Maganar gaskiya ita ce: Acikin Shekaru sama da 50 da aka shafe ana sanya Tafsiran Malamai agidajen Radio, da kuma Shekaru sama da 100 da akayi ana gudanar da tafsir a Masallatanmu na Qasar hausa, Zamu iya cewa MUN SAMU QARUWAR MASANAN ILIMIN ADDINI, AMMA KUMA MUN SAMU RAGUWAR MASU AIKI DA ILIMIN.
Idan mun kalli yanayin da al'ummarmu suke ciki ayanzu mun kwatantashi da shekaru talatin ko arba'in da suka gabata, zamu ga cewar:
- ZUMUNCI YAYI QARANCI.
- AMANA TAYI QARANCI.
- GASKIYA TAYI QARANCI.
- ADALCI YAYI QARANCI.
- LADABI DA BIYAYYA SUNYI QARANCI.
Mutane bassu damuwa sosai don sunji kana Wa'azi, ba zasu fara yi maka kabbara ba, sai sunji ka fara "RAGARGAZA". Wato sai sunji ka fara zagin wasu Malaman, ka fara kafirta wasu Jama'ar... Daga nan zakaji RUWAN KABBARA!!! (SUBHANALLAH).
Shi Wa'azi ba ya zama mai amfani har sai idan mai yinsa ya fara Wa'azantar da kansa kafin ya Wa'azantar da waninsa.
Kuma kalmar WA'AZI bata zama mai amfani awajen Allah, sai wacce aka furta domin Allah da Manzonsa (saww). Shima Ilimi komai yawansa ba zai zama mai amfani ba, har sai idan an nemoshi ne tun farko domin Taimakon Allah da Manzonsa da addininsa. Ba don neman suna, ko neman Girma, ko neman abin duniya, ko kuma domin nemqn jayayya da wasu jama'a ba.
Duk wanda ya tara ilimi don yin jayayya da mutane, to wannan ilimin nasa shine zai zama Linzamin da za'a jashi dashi zuwa wutar Jahannama.
DAGA ZAUREN FIQHU.