A yayinda wasu 'yan Nigeria ke ci gaba da toba bakon albarkacinsu akan batun cire tallafin mai, tsohon shugaban Nigeria Janaral Yakubu Gowon shima ya tofa bakin albakarcinsa akan wanna batu. Tsohon shugaban yana goyon bayan a cire tallafin mai
A yayinda wasu 'yan Nigeria ke ci gaba da fadin albarkacin bakinsu akn batun cure tallafin mai.
Tsohon shugaban Nigeria Janaral Yakubu Gowon shia ya baiyana ra'ayinsa akan wannan batu. A wata hira da Aliyu Mustapha yayi dashi, Janaral Gowon yace a lokacinda yake jan ragamar mulkin Nigeria, akwai lokacinda wasu 'yan jarida suka zargin gwamnatinsa da laifin yin barna da kudin Nigeria.
Yace ya maida martani da cewa Nigeria tana da kudi, amma ba wai kudin da ake dashi bane, wani irin amfani ne da za'a yi da kudin saboda a gyra sha'anin tattalin arzikin kasa da kuma biyan bukatun Nigeria.
Yace cire tallafin mai zai taimaka wajen kawar da zamba