Hukumomi a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nigeria sun ce mutane 69 sun mutu lokacin da wata tankar mai ta kife a wata tashar mota da ke birnin Onitsha .
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi inda mutane 69 suka kone kurmus a lokacin da tanker ta kwacewa direban a yayinda ya shawo gangara inda wasu motocin 12 suma suka kone.
A yanzu haka wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu suna samun kulawa a asibiti sakamakon kuna.
Hadarin dai yayi muni sosai inda mutane a yankin suka shiga cikin damuwa a yayinda wasu rahotanni suka ce gwamnan jihar Anambra Willie Obiano, ya yi kuka a lokacin da ya ziyarci wurin saboda yadda ya ga gawawwakin mutane a kone.
Ana yawan samun munanan hadura a kan titunan Nigeria.