TAMBAYA TA 1640
********************
Assalamu Alaikum malan ya Azumi da fatar kasha ruwa lfy malan ni Coper ne (mai hidimar kasa) a lodge din da muke maza da mata dakuna daban.
To akwai wata daga cikin matan tun da muka fara Azumi da ita mukeyi kuma bata Sallah. Ko daman chan kafin Azumi ban taba ganin tayi Sallah ba. Na bincika Iyayenta suna Sallah yarabawa ne. (YORUBA) munce ta zan ki yin Sallah, ta kiyi malan dan Allah ka taimaka mana da shawara. Kuma yaya matsayin Azumin ta. Assalamu Alaikumu.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Hakika Sallah ita ce rukuni mafi girma daga cikin rukunan Musulunci bayan kalmar shahada.
Saboda muhimmancinta, Allah ya umurcemu da yinta agurare fiye da talatin acikin Littafinsa mai girma. Kuma Manzon Rahama (saww) ya nuna muhimmancinta sosai acikin hadisai da dama.
Manzon Allah (saww) yace: "ABINDA KE TSAKANIN MUTUM DA TSAKANIN SHIRKA DA KAFIRCI, SHINE BARIN YIN SALLAH".
(Imam Muslim ne ya ruwaito).
Awani hadisin kuma yace: "SALLAH ITA CE GINSHIKIN ADDINI. DUK WANDA YA TSAYAR DA ITA, TO HAKIKA YA TSAYAR DA ADDINI. DUK WANDA KUMA YA BAR YIN TA, TO HAKIKA YA RUSHE ADDINI".
To idan mun dubi abinda hadisan nan suka Qunsa, to hakika zamu tabbatar da cewa ita wannan Baiwar Allah din tana cikin hadari akan addininta.
Ya kamata kuja hankalinta sosai. Kuyi mata nasiha ku gaya mata In dai tana yin azumin ne domin samun lada awajen Allah, to hakika Azumin ba zai amfaneta ba, har sai tana yin sallah. Kuma sallah ita ce farkon abinda za'a duba acikin ayyukan kowanne mutum.
Daga karshe muna yi muku addu'a da fatan Allah ya taimakeku, Allah shi Qara mana riko da addininmu aduk inda muka tsinci kanmu.
WALLAHU A'ALAM.