Assalam ya malam inada tambaya kamar haka;
Misali ni birkilane kuma na kasance musulmine sai aka ban contrc din gini na church, ogana yace mu zamuyi.
Yaya matsayin mu yake idan munyi wannan aikin ???
(Daga Khamis Isah).
AMSA.
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa malamai sunyi bayani cewa:
Baya halatta musulmi yazama Birkila a Chochi, saboda hakan yana daga cikin taimakawa aikata zunubi, kuma zai iya jawowa mutum yaga yadda ake shirka da Allah, wanda hakan zai iya masa tasiri.
Allah madaukakin sarki yana cewa:
"kada kuyi taima kekeniya wajen aikata sa6o"
"Surah Al-ma'idah ayata: 2.
Sannan duk abinda yake kaiwa zuwaga barna, to zai zama haramun ko makaruhi.
Amma zaka iya taimakon christer idan ya bukataci taimakon, addinin muslunci bai hanaka ba.
Saidai ba'a yardar maka akan addininsaba, kamar yadda shima bazai taimakeka akan naka ba.
Don neman kari bayani sai aduba: Al'umm ta Shafi'i 4/213.
Allah shine mafi sani.
Domin kasancewa damu akoda yaushe.