TAMBAYA TA 1633
*********************
Assalamu alaikum malam Dan Allah ina da tambaya ne mace ce mijinta ya taba mata saki 2 sai suka kara samun sabani sai yace in ta fita a bakin aurenta. kuma sai ta fita. Shin yaya matsayin aurensu? sannan kuma har ta gama idda daga baya wani yake gaya mishi aurensu zai gyaru. toh malam idan auren su zai gyaru ta wacce hanya za'a gyara??
(Daga Dalibin Zauren fiqhu Whatsapp 2)
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa Rahmatullah. Hakika wannan maganar da ya fada, da kuma abinda ta aikata ya sanya sakin dake tsakaninsu sun zama guda uku kenan.
Kuma Saki ne guda uku daban daban. Don haka babu sabani tsakanin malamai cewa wannan auren ba zai gyaru ba, har sai ta auri wani Mijin, sun zauna zaman aure har ya sadu da ita. Cikakkiyar saduwa wacce babu wata shubuha acikinta.
To idan shi wannan Mijin nata na biyu ya saketa, sannan ta zama halal ga wancan na farko zai iya zuwa ya nemi aurenta bayan ta gama iddah kenan. Idan ta yadda ta sake aurensa tare da sabon sadaki.
Allah yana cewa:
"IDAN YA SAKETA (SAKI NA UKU KENAN) TO BATTA HALATTA GARESHI DAGA BAYA HAR SAI TA AURI WANI NAMIJIN BANDA SHI..
IDAN SHI (MIJINTA NA BIYUN) YA SAKETA, TO BABU LAIFI GARESU SU KOMA (CIKIN AURE) IDAN SUNA TSAMMANIN ZASU IYA TSAYAR DA DOKOKIN ALLAH".
(Suratul Baqarah ayah ta 230).
Al Imam Ibnu Katheer yayi dogon bayani akarkashin fassarar wannan ayar. Daga ciki yana cewa:
"Abind ake nufi shine idan mutum ya saki matarsa, saki na uju bayab ya riga yayi mata saki biyu tun farko, To hakika ita ta haramta gareshi har sai bayan ta auri wani namijin bayan shi. Kuma har sai shi wannan mijin yayi Jima'i da ita acikin Sahihin aure.
Da ace wani zai sadu da ita ba ta hanyar aure ba, koda ta hanyar mallaka ne, to batta halatta ga Mijin nata na farko. Tunda wannan wanda ya sadu da ita din ba mijinta bane.
Hakanan da ace zata yi aure, amma su rabu da mijin tun jafin saduwa, to duk da haja batta halatta ga mijinta na farko".
Acikin wannan bayani zamu fahimci cewa babu wata hanyar gyaran auren nan har sai taje tayi wani auren. Bisa sharadin cewa bata yishi don neman halattuwa ga mijinta na farko ba.
Amma idan tayi auren kisan wuta, to HAR ABADA ba zata halatta ga Mijinta na farko din ba. Kamar yadda ruwayoyi Sahihai suka tabbata daga Abdullahi bn Mas'ud, Unar bn Khattab, Abdullahi bn Umar, Abu Hurairah, Aliyu bn Abi Talib, da sahabbai masu yawa (Allah shi yarda dasu baki daya).
Shi wancan da yace za'a iya gyara auren, sai a tambayeshi ya jawo hujjah... Don Allah Ya kamata mutane su dena tsoma baki acikin sha'anin addini mutukar ba hujjah garesu daga Alqur'ani da hadisin Manzon Allah (saww) ba.
WALLAHU A'ALAM.